NI BA HATSARI NE GA AL'UMMAR KASARNAN BA!, FADIN JAGORAN SHI'A A NIGERIA.
— Sheikh Ibraheem Zakzaky (H):
"Nake ce musu, da suke cewa ni hadari ne, misali, to mu gwada mana. Yanzu na san ni zan iya shiga kasuwa na je na yi cefane na fita lafiya lau, amma na san da kyar zan fita kasuwar saboda mutane za su yi ta zuwa suna son mu gaisa. To amma wani Kantoma ko wani Gwamna (ko Ciyaman ko Shugaban kasa) ya je ya shiga kasuwa ba tare da dan sanda ba mu gani. Ya je ya shiga kasuwa shi kadai in bai sha duwatsu ba! Saboda mutane sun san barawo ne, macuci. Ka ga in sun ce ni hadari ne, to ba hadari ne ga mutane ba. Hadari ne ga 'yan fashi, masu mallakar kasa da bakin bindiga. Suna ganin ni hadari ne saboda za su rasa mutane. Sai su ce zai ta da hankali! Hankalin wane ne zai tashi? Na mutanen gari ko na mahukuntan kasa? In na mahukunta ne to dama su basu son gaskiya dole gaskiya ta tada musu hankali."
— Shaikh Ibraheem Zakzaky a wani jawabinsa a garin Potiskum shekarun baya.

Comments
Post a Comment