Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali
Tawagar wakilan ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gana da shugaban Mali Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane da sojoji suka haɓarar a ranar Litinin.
A yayin ganawar hamaɓararren shugaban ƙasar na Mali da Firaministan sun sanar da yin murabus a gaban wakilan Ecowas da na Tarayyar Afrika da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
Majiyoyi sun ce sojoji ne suka tilasta masu yin murabus.
A ranar Talata Kanal Assimi Goita -wanda sh ya jagoranci juyin mulkin bara ya ba da sanarwar cewa ya tsige shugaban kasa da Firaminista.
Ya zarge su da yin zagon kasa ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta hanyar naɗa sabbin ministocin ba tare da tuntubar sojoji ba.
Ecowas da Tarayyar Turai na duba yiwuwar ƙaƙaba takunkumi kan sojojin da suka yi juyin mulkin.
Nan gaba a yau ne Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan rikicin siyasar ta Mali.
Islamicnewupdate.com
Comments
Post a Comment