Sojojin Najeriya sun ce sun kama masu kai wa Boko Haram man fetur

 

Sojojin Najeriya sun ce sun gano wasu wuraren da ake zargin mayaƙan Boko Haram ke ajiyar kayayyaki a garin Kurkareta a jihar Yobe.

Sanarwar da kakakin rundunr Mohammed Yarimaya fitar ta ce dakarun rundunar Hadin Kai ta kai samame a ranar Talata inda ta ƙwato jarkokin fetur 62 a gidaje da shagunan da Boko Haram ke ɓoye kaya.

Sannan dakarun rundunar sun kuma ƙwato motoci uku da wasu mutanen da ake zargin suna kai wa ƙungiyar Boko Haram kaya.

Sojojin sun ce sun kai samamen ne bayan samun bayanai daga mutanen gari da suka kwarmata masu bayanai.

Sai dai rundunar ba ta wallafa hotuna ko bidiyon kayayyakin da ta ce ta ƙwato ba kamar yadda ta saba.

Islamicnewupdate.com

Comments

Popular posts from this blog

Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali

دعاء المشلول‌

Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa