SHAFI (1) ABUBUWAN DA ZA MU KOYA DAGA RAYUWAR SAYYADA ZAHRA (AS)
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon rahama Muhammad dan Abdullahi da Iyalan gidansa tsarkaka, taurarin duniya da lahira da Sahabbansa managarta.
Nazari da bincike a kan rayuwar Sayyadah Zahra abu ne faffada ainun, wanda za mu iya misalta shi da iyo a teku. Amma za mu yi ne da nufin bijiro da yadda rayuwarta ta kasance don daukar darussan da ke cikinta, haka kuma don mu sanya ta a matsayin samfuri ga rayuwar Musulmi baki daya. Ta yadda za mu fahimci manufar rayuwarmu wadda domin ta ne Allah ya halicci dan Adam.
An haifi Fatimatuz Zahra ne ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Thani a shekara ta biyar bayan wahayi. Mahaifinta shi ne Manzon Allah Muhammad dan Abdullahi, cikamakon Annabawa da Manzanni, rahama ga talikai. Mahaifiyarta kuwa ita ce; Nana Khadijatul Kubra (AS) matar Manzo (S) ta farko, wacce ta fara amsa kiran Manzo. Sannan kuma ta bai wa wannan addini muhimmiyar gudummawar da ba za a taba mantawa da ita ba har abada. Manzo (S) ya ce: “Wannan addini bai tabbata ba sai da dukiyar Khadija da takobin Ali da kariyar Abu Talib.”
Allah (T) ya yi wa Sayyidah Zahra baiwa da karamomin da ba za su kirgu ba. Tun asali ta zama fansa ga Mahaifinta daga gorin da mushirikai suke masa na ganin sa a matsayin mai yankakken baya. Shi ne Allah (T) ya ba shi Fatima (AS) kamar yadda ya zo a Suratul Kauthar. Sannan Sayyidah Zahra ta zama tsarkakakken tsatso daga tataccen rowan tuffah daga Aljanna, ta yadda har ma Manzon Allah (S) yana cewa idan ya so ya ji kamshin Aljanna yakan sumbaci Fatima ne. Kana ga shaidar sauki da rashin fargaba da zullumi da Nana Khadija ta bayar wajen daukar cikin Fatima (AS). Sannan ga magana da hira da ta gudana tsakaninta da Sayyidah Zahra tun tana cikin, kamar yadda ya zo a littafin Imamu Shafi’i da Dahlawiy. Kana ga mataye hudun da suka zo daga Aljanna don taya ta hidimar haihuwarta, inda ta zo duniya tana mai sujada ga Allah (T) tana mai daga yatsunta zuwa sama. Manzo ya yi farin ciki da wannan abar haihuwa, ya sa mata suna Fatima bisa wahayi daga Allah (T).
Cikin ikon Allah Sayyidah Zahra ta rika girma da gama-garin yara ke yi a wata ruwayar cikin sati daya. baya ga wannan suna tana da sunaye da yawa saboda girmanta da kuma daukakarta, kamar yadda ake cewa; “yawan sunaye na nuni ga girman mai su.”
Nana A’isha ta ce ba wanda ya yi kama da Manzon (S) a zamansa da tafiyarsa da zancensa kamar Fatima (AS).” Manzo (S) ya nuna matukar kauna ga wannan ’ya tasa. Yana yarda da yardarta, kuma yana fushi da fushinta, har ma ya yi nuni da cewa duk abin da ya same ta, to ya same shi ne kai tsaye da fadinsa; “Fatima tsoka ce daga gare ni, wanda ya bata mata, hakika ya bata min.” Kuma ya ce: “Fatima Allah na fushi da fushinta, yana yarda da yardarta.” To a nan za mu gane irin daukaka da matsayin da Allah (T) ya yi mata.
Zamu cigaba insha Allah
Follow and share
Comments
Post a Comment