Posts

Showing posts from January, 2022

SHAFI (1) ABUBUWAN DA ZA MU KOYA DAGA RAYUWAR SAYYADA ZAHRA (AS)

Image
  Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon rahama Muhammad dan Abdullahi da Iyalan gidansa tsarkaka, taurarin duniya da lahira da Sahabbansa managarta. Nazari da bincike a kan rayuwar Sayyadah Zahra abu ne faffada ainun, wanda za mu iya misalta shi da iyo a teku. Amma za mu yi ne da nufin bijiro da yadda rayuwarta ta kasance don daukar darussan da ke cikinta, haka kuma don mu sanya ta a matsayin samfuri ga rayuwar Musulmi baki daya. Ta yadda za mu fahimci manufar rayuwarmu wadda domin ta ne Allah ya halicci dan Adam. An haifi Fatimatuz Zahra ne ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Thani a shekara ta biyar bayan wahayi. Mahaifinta shi ne Manzon Allah Muhammad dan Abdullahi, cikamakon Annabawa da Manzanni, rahama ga talikai. Mahaifiyarta kuwa ita ce; Nana Khadijatul Kubra (AS) matar Manzo (S) ta farko, wacce ta fara amsa kiran Manzo. Sannan kuma ta bai wa wannan addini muhimmiyar gudummawar da ba za a taba mantawa da ita ba har abada. Manzo (S) ya ce...

HAIHUWAR SAYYIDA FATIMA AL-ZAHRA (A.S)

Image
An haifi Fatima al-Zahra (a.s) ne a ranar juma'a, Ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi. Bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w.a) ya amshi 'yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna  Fatima . An haifeta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi'u daga Khadija. Fatima ta kasance mai dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi'unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, har ma A'isha ta taba cewa: "Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (s.a.w.a) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima 'yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (s.a.w.a) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta (1) " Allah Ya so Fatima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntat...

Sheikh Zakzaky (H) Ya Baiyanawa Duniya Manufarsa.

Image
 “Sheikh Zakzaky (H) ya bayyanawa Al'ummah cikakken saƙon da'awarsa kamar haka.... ” “Kamar yadda Bature baiyi mana wayo ba, yace kafirci ya komar damu to muma musulunci zamu koma”.  “Musulunci daman Shine  jinin mu shine gadon mu  shine alfaharin mu”.  “Tayi wu wani yace Ohoo! To zaka 6alle  arewa ne?  Sae muce aa mu musulunci muka ce maka xamuyi, musulunci kuma ba ruwanshi da kudu ba ruwanshi da arewa”.    “Musulunci a wajensa addini ne na Allah duka  kasa  kuma ta Allah ce”.  —Sheikh zakzaky (H). Islamicnewupdate.com

“JUYIN JUYA HALI NE MAFITA, BA CANJIN GWAMNATI BA!”.

Image
  –Shaikh zakzaky (H) “Canja Gwamnati ta hanyar katin zave ba shi ne mafita na halin quncin rayuwa da  ake ciki ba, kullum aka samu sabon shugaba sai an ce gara na baya da shi, kuma hakan zai  ci gaba muddin ba mun canza tsarin bane. Kamar mota ce ta riga ta lalace, injinta ya  buga, sai ka ce ai direban ne bai iya tuqi ba, ka cire wannan ka sanya wancan, to, in ba  ka gyara motar ba ne, babu yadda za a yi ta koma daidai, saboda ainihin lamarin ba  direban ba ne, motar ce! Dan haka, qasar nan tana buqatar ‘Juyin Juya Hali ne’ ba  ‘Canjin Gwamnati ba!”. –Shaikh zakzaky (H)

Bauchi opens N330m new general hospital

Image
map of bauchi state The Chairman of the Board of Trustees of the Peoples Democratic Party, Walid Jibrin, on Wednesday, inaugurated the newly-constructed Dambam General Hospital, constructed by the Bauchi State government at the cost of N330 million. Speaking while inaugurating the project, Jibrin commended the state governor, Bala Mohammed, for his achievements in various sectors since his assumption of office in 2019. He said, “I believe Bauchi State will never go backwards again. I want to appeal to the people of Bauchi State to give the governor their maximum support and cooperation always. “It is my belief that this hospital that we are inaugurating today will not only be a place of treatment of the sick, but a centre for training nurses and midwives. I hope that in future, it will be a centre for training of young doctors. “I commend Bauchi State governor for providing this hospital for the improvement of the health of the state, believing that this hospital will meet the needs of...

Police begin probe as gunmen storm APC meeting, kill two in Enugu

Image
  Scene of the incident Obeagu Awkunanaw community, in the Enugu South Local Government Area of Enugu State, has been thrown into mourning after gunmen on Tuesday killed two chieftains of the All Progressives Congress, including the state youth leader, Kelvin Ezeoha. The gunmen reportedly invaded a meeting being held by members of the Ward 3 Obeagu Awkunanaw around 6.30pm, killing the two party chieftains. Another party member was abducted by the hoodlums. Sources said the meeting, which was to reconcile members from the two factions of the party, was ongoing when the gun-wielding men, numbering over seven, stormed the gathering and unleashed mayhem. The Enugu State chapter of the APC had been battling a leadership crisis for some years. However, all hopes to resolve the crisis during the ward, local and state congresses were dashed, as two parallel leaders emerged at the end of the exercise. While former state Commissioner for Works, Ugochukwu Agbala, emerged as the chairman of a ...

Sojojin Najeriya sun ce sun kama masu kai wa Boko Haram man fetur

Image
  Sojojin Najeriya sun ce sun gano wasu wuraren da ake zargin mayaƙan Boko Haram ke ajiyar kayayyaki a garin Kurkareta a jihar Yobe. Sanarwar da kakakin rundunr Mohammed Yarimaya fitar ta ce dakarun rundunar Hadin Kai ta kai samame a ranar Talata inda ta ƙwato jarkokin fetur 62 a gidaje da shagunan da Boko Haram ke ɓoye kaya. Sannan dakarun rundunar sun kuma ƙwato motoci uku da wasu mutanen da ake zargin suna kai wa ƙungiyar Boko Haram kaya. Sojojin sun ce sun kai samamen ne bayan samun bayanai daga mutanen gari da suka kwarmata masu bayanai. Sai dai rundunar ba ta wallafa hotuna ko bidiyon kayayyakin da ta ce ta ƙwato ba kamar yadda ta saba. Islamicnewupdate.com

Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali

Image
  Tawagar wakilan ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gana da shugaban Mali Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane da sojoji suka haɓarar a ranar Litinin. A yayin ganawar hamaɓararren shugaban ƙasar na Mali da Firaministan sun sanar da yin murabus a gaban wakilan Ecowas da na Tarayyar Afrika da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya. Majiyoyi sun ce sojoji ne suka tilasta masu yin murabus. A ranar Talata Kanal Assimi Goita -wanda sh ya jagoranci juyin mulkin bara ya ba da sanarwar cewa ya tsige shugaban kasa da Firaminista. Ya zarge su da yin zagon kasa ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta hanyar naɗa sabbin ministocin ba tare da tuntubar sojoji ba. Ecowas da Tarayyar Turai na duba yiwuwar ƙaƙaba takunkumi kan sojojin da suka yi juyin mulkin. Nan gaba a yau ne Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan rikicin siyasar ta Mali. Islamicnewupdate.com Article share tools View more share options Share this post Copy this l...

Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa

Image
  Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari Sheikh Ibrahim Maqari na daga cikin malaman da kwatakwata ba sa goyon bayan malamai su shiga fagen siyasa ko kuma su sa baki. A wata fatawa da malamin ya bayar wadda aka naɗa a bidiyo, ya bayyana cewa ya kamata a raba tsakanin siyasa da da'awa, yana cewa "ɗan siyasa daban malamin addini daban". "Idan malamin addini yana so ya sa baki a siyasa ya cire hular addini ya koma honarabul ya yi magana cikin siyasa. Idan ba haka ba to mambarinsa haƙƙin Allah ne, mambarinsa wakilcin Allah da Manzon Allah yake yi, kada ya yaudari al'umma," in ji Sheikh Maqari. Sheikh Maqari ya kuma bayyana cewa "duk mutumin da ya ƙara zuwa zai tallata muku wani to ku ba shi sharaɗi; ya ɗauki Al-Kur'ani ya rantse ba a ba shi ko kobo a duhu ba, ya karɓi Al-Kur'ani ya rantse ba kwangila ya karɓo ba, ya rantse da Allah wanda ya halicce shi babu wanda ya biya shi wannan abin da yake yi". A cewarsa: "Idan zai iya wannan rantsuwar, wato abi...

Ce-ce-ku-ce ya barke kan dacewa ko rashin dacewar shigar malaman addini siyasa

Image
  Batun shigar malaman addinin Musulunci siyasa ya kwana biyu yana jawo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya. A zaɓukan da aka yi na baya a ƙasar, an ji yadda malamai daban-daban suka fito suka bayyana ra'ayoyinsu kan wasu 'yan takarar siyasa, lamarin da ake ganin ya jawo rashin jituwa tsakanin wasu ɓangarorin. Ya danganta da fahimtar da kowa yake yi wa malaman addini kan ra'ayinsu na siyasa. Wasu na yi musu fahimta cewa suna lallashin mabiyansu don su zaɓi mutumin kirki da ziummar a samu ci gaba mai ɗorewa a ƙasa. Wasu kuma na ganin cewa akwai malaman da suna yi ne domin ra'ayin ƙashin kansu, watakila domin biyan wata buƙata tasu ko ta ƙungiyarsu. Wasu malaman kan yi hannunka mai sanda a wajen wa'azi domin jawo ra'ayin jama'a kan wanda za a zaɓa, wasu kuma kan fito ɓaro-ɓaro su kama sunan ɗan siyasa a cikin masallaci ko kuma a wurin wa'azi domin nema masa ƙuri'a. Ganin cewa an kaɗa gangar siyasar 2023 a Najeriya, tuni wasu malaman suka soma kama s...