Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa

 Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari


Sheikh Ibrahim Maqari na daga cikin malaman da kwatakwata ba sa goyon bayan malamai su shiga fagen siyasa ko kuma su sa baki.

A wata fatawa da malamin ya bayar wadda aka naɗa a bidiyo, ya bayyana cewa ya kamata a raba tsakanin siyasa da da'awa, yana cewa "ɗan siyasa daban malamin addini daban".

"Idan malamin addini yana so ya sa baki a siyasa ya cire hular addini ya koma honarabul ya yi magana cikin siyasa. Idan ba haka ba to mambarinsa haƙƙin Allah ne, mambarinsa wakilcin Allah da Manzon Allah yake yi, kada ya yaudari al'umma," in ji Sheikh Maqari.

Sheikh Maqari ya kuma bayyana cewa "duk mutumin da ya ƙara zuwa zai tallata muku wani to ku ba shi sharaɗi; ya ɗauki Al-Kur'ani ya rantse ba a ba shi ko kobo a duhu ba, ya karɓi Al-Kur'ani ya rantse ba kwangila ya karɓo ba, ya rantse da Allah wanda ya halicce shi babu wanda ya biya shi wannan abin da yake yi".

A cewarsa: "Idan zai iya wannan rantsuwar, wato abin da ya yi imani da shi ne yake kiran ku zuwa gare shi, to Allah ya ba da sa'a. Amma kada ku ci gaba da bari ana yaudarar ku, ana amfani da wani sauti da kuke ji, ana kwasar ku ana cinikin ku ana sayar wa 'ƴan siyasa da ku kuma alhalin kuɗin nan shi da ƴaƴansa zai je ya amfana."

Wannan itace maganar daya fadamasu da kuma shawarwari daga Limamin babban masallacin abuja.

Allah bamu nasara labari daga 

Islamicnewupdate.com

Comments

Popular posts from this blog

Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali

دعاء المشلول‌