Ce-ce-ku-ce ya barke kan dacewa ko rashin dacewar shigar malaman addini siyasa
Batun shigar malaman addinin Musulunci siyasa ya kwana biyu yana jawo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya.
A zaɓukan da aka yi na baya a ƙasar, an ji yadda malamai daban-daban suka fito suka bayyana ra'ayoyinsu kan wasu 'yan takarar siyasa, lamarin da ake ganin ya jawo rashin jituwa tsakanin wasu ɓangarorin.
Ya danganta da fahimtar da kowa yake yi wa malaman addini kan ra'ayinsu na siyasa. Wasu na yi musu fahimta cewa suna lallashin mabiyansu don su zaɓi mutumin kirki da ziummar a samu ci gaba mai ɗorewa a ƙasa.
Wasu kuma na ganin cewa akwai malaman da suna yi ne domin ra'ayin ƙashin kansu, watakila domin biyan wata buƙata tasu ko ta ƙungiyarsu.
Wasu malaman kan yi hannunka mai sanda a wajen wa'azi domin jawo ra'ayin jama'a kan wanda za a zaɓa, wasu kuma kan fito ɓaro-ɓaro su kama sunan ɗan siyasa a cikin masallaci ko kuma a wurin wa'azi domin nema masa ƙuri'a.
Ganin cewa an kaɗa gangar siyasar 2023 a Najeriya, tuni wasu malaman suka soma kama sunayen wasu 'ƴan takara da kiran a zabe su.
Dangane da wannan batu, BBC ta tuntuɓi wasu malaman Musulunci da kuma nazarin fatawowin da wasu malaman suka bayar dangane da ra'ayin siyasa.
Bisa nazarin da BBC ta yi, malaman sun kasu gida uku, wasu na goyon bayan malamai su shiga siyasa, wasu kuma ba sa goyon baya, inda wasu kuma suka ce sun tsaya a tsakiya.
islamicnewupdate.com
Comments
Post a Comment