An haifi Fatima al-Zahra (a.s) ne a ranar juma'a, Ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi. Bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w.a) ya amshi 'yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Fatima . An haifeta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi'u daga Khadija. Fatima ta kasance mai dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi'unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, har ma A'isha ta taba cewa: "Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (s.a.w.a) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima 'yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (s.a.w.a) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta (1) " Allah Ya so Fatima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntat...