WAFATIN UMMUL BANIN MAHAIFIYAR ABUL FADLIL ABBAS!
Bismillahirrahmanirrahim
13 ga Watan Jumadat-Thaniyah.
A irin wannan rana ce a Shekara ta 65 bayan hijirah, a ranar Juma'a, Allah ya karbi ran Ummul Banin (S.A), Mata a wajen Imamu Ali alaihissalam kuma Mahaifiyar Abul Fadlil Abbas Jarumin Karbala!.
Tsarkakken Makwancinta yana nan a ciki Makabartar Baqi'a, a kusurwar bangaren hagu kusa da Makwancin Sayyid Ibrahim Dan Ma'aiki (Saww), da Zainab da Ummul Kulthum da Abdullahi da Kasim, amincin Allah ya kara tabbata a gare Su.
WACE CE UMMUL BANIN (S.A)?
Zanannen Sunanta Shi ne Fadimatu 'Yar Hizam.
Mahaifiyarta kuwa ita ce: Thumamah bnt Sahal bn Amir bn Malik bn Ja'afar bn Kilab.
Ta kuma Shahara da Lakabin Ummul Banin, kuma an ce Imamu Ali (as) ne da kansa ya kira ta da laqabin na Ummul banin.
AURENTA DA IMAMU ALI (AS).
Malaman Tarikhi sun ruwaito cewa Imamu Ali (as) ya sanya Dan uwansa Aqil ne da ya nemo masa wata Mace Jaruma daga Gidan Jarumawan Kabilun Larabawa domin ta haifa masa Jarumin da zai agaza wa Dansa Husain (as) a Karbala.
Da yake Aqeel Allah ya hore masa ilimin sanin Nasabar Gidajen Larabawa da Tarihinsu, kuma Mutum ne mai kaifin hankali da hazaqa ta ban al'ajabi a wannan janibin!. Shi ne ya Shawarci Imam (as) kan ya auri Wannan baiwar Allah mai girman matsayi da daraja.
Ta kuma haifa wa Imam (as) 'Ya'Ya hudu Maza: ABBAS, ABDULLAHI, JA'AFAR da UTHMAN.
Haifar Wadan nan Gwarazan 'Ya'Ya hudu Maza ne ya sa aka kira ta Ummul Banin, wato Mahaifiyar 'Ya'Ya Maza. Kuma dukan Su, Su hudun Sun yi Shahada ne tare da Dan Uwansu Imamu Husain (as) a Waki'ar Karbala mai radadi!.
Littafin Umdatud-Daalib, Shafi na 357 .
SON TA, DA KUMA KARFIN WILAYARTA GA LIMAMIN ZAMANINTA IMAMU HUSAIN (AS).
Malaman Tarikhi sun ambata cewa: A lokacin da Labarin Kashe Imamu Husai (as) ya sami Mutanen Madina, Ummul banin (S.a) ta fito a cikin yanayi na tsananin bakin ciki!, tana cewa ina Husain!?
Aka ce da ita: Allah ya girmama Ladanki kan Danki Abbas!!.
Ta ce: Ba Abbas na tambaye ku ba, ina Husain!?.
Aka ce da ita: Allah ya girmama Ladanki kan Danki Uthman!.
Ta ce: Husaini nake Tambayar Ku!?
Aka ce da ita: Allah ya girmama Ladanki kan Danki Ja'afar!.
Ta ce: Ina Husain!?
Aka ce da ita Allah ya girmama Ladanki a bisa rashin Danki Abdullah!!
Ta ce: Husain na ke tambayar Ku!?
Sai aka ce da ita: An kashe Husain a Karbala!!. Sai ta fadi tana Sumammiya!! (S.A)!
An ruwaito cewa ma: Ta kan yi Kukan Imamul Husain (as) da yanayi mai daga hankali da ban tausayi!, ba ma iya Mutanen kirki ba, a'a har irin su Marwan bn Hakam su kan yi Kuka kan yanayin Nudban kukan Imamu Husain (as) da take yi a Makabartar Baqi'ar Ma'aiki (Saww) da ke garin Madina.
Littafin Maqatilud-Dalibiyyin, na Isfahaniy, Shafi na 85.
Ko shakka babu cewa Ummul Banin (S.A) ta kasance mai girman Matsayi da daraja a wajen Allah Swt, domin kuwa ita ce take ragewa Imamu Ali (as) kewar Rabuwa da Sayyida Az-Zahrah (S.A), kuma ta kasance mai fifita 'Ya'Yan Sayyida (S.A) a kan nata 'Ya'Yan. Ta kasance tana sanar da 'Ya'Yanta cewa: Ba daidai Kuke da Hasan da Husain da Zainab ba, Ku mutu a wajen kare Su.
Kuma ta kasance mai hakuri da juriya da dakewa a tafarkin Allah Swt, hakan ya sa ma ake samun ijaba da gaggawa idan aka yi Tawassuli da ita a cikin Kowacce irin Bukata, musamman ma ya zama an yi bakance ne da zimmar cewa idan Bukata kaza.. ta biya za a yi aikin Alkhairi kaza...Ladar a kai ga Ummul Banin (S.A), kamar yanda Jagora Sayyid Zakzay (H) ya taba yin ishara da hakan a cikin Karatuttukan Su masu Albarka.
Amincin Allah ya kara tabbata a gare ki ya Ummal Banin, wa rahmatullahi wa barakaruh.
ZIYARAR UMMUL BANIN (S.A):
أَشهَدُ أَن لا إلهَ إلا الله وَحدَهُ لاشَرِيكَ لَهُ، وَأَشهَدُ أنَّ مُحَمَّدَاً عَبدُهُ وَرَسُولُهُ، السَّلامُ عَلَيكَ يَا رَسُولَ الله، السَّلامُ عَلَيكَ يَا أَمِيرَ الُمؤمِنين، السَّلامُ عَلَيكِ يَا فَاطِمَةَ الزَّهرَاءِ سَيِّدَةِ نِسَاءِ العَالَمِين، السَّلامُ عَلَى الحَسَنِ وَالحُسَينِ سَيِّدي شَبَابِ أَهلِ الجَنَّة، السَّلامُ عَلَيكِ يَازَوجَةَ وَصِيِّ رَسَولِ الله، السَّلامُ عَلَيكِ يَا عَزِيزَةَ الزَّهرَاءِ عَلَيهَا السَّلام، السَّلامُ عَلَيكِ يَا أُمَّ البُدُورِ السَّوَاطِع فَاطِمَةَ بِنت حزَام الكلابيّة، المُلَقَّبةُ بِأُمّ البَنِين وَبَاب الحَوَائِج، أُشهِدُ اللهَ وَرَسُولهُ أَنَّكِ جَاهَدتِ في سَبِيلِ اللهِ، إِذ ضَحّيتِ بِأَولَادَكِ دُونَ الحُسَين بنَ بِنتِ رَسُولِ الله، وَعَبَدتِ اللهَ مُخلِصَةً لَهُ الدِّين بِولائكِ لِلأَئِمَّةِ المَعصُومِين عَلَيهمُ السَّلام، وَصَبَرتِ عَلَى تِلكَ الرَزيَّةِ العَظِيمَةِ، وَاحتَسَبتِ ذَلِكَ عِندَ الله رَبّ العَالَمين، وَآزَرتِ الإمَامَ عَليَّاً في المِحَنِ وَالشَّدَائِدِ وَالمَصَائِب، وَكُنتِ في قِمَّةِ الطَّاعَةِ وَالوَفَاء، وَأنَّكِ أَحسَنتِ الكَفَالَة وَأَدَّيتِ الأَمَانَة الكُبرى في حِفظِ وَديعَتَي الزَّهرَاء البَتُول الحَسَنِ وَالحُسَينِ وَبَالَغتِ وَآثَرتِ وَرَعَيتِ حُجَجَ اللهِ المَيَامِين، وَرَغبتِ في صِلَةِ أَبنَاء رَسُولِ رَبِّ العَالَمين، عَارِفَةً بِحَقِّهِم، مُؤمِنَةً بِصِدقِهِم، مُشفِقَةً عَلَيهِم، مُؤثِرَةً هَوَاهُم وَحُبَّهُم عَلَى أَولَادكِ السُّعَدَاء، فَسَلامُ اللهِ عَلَيكِ يَا سَيِّدَتي يَا أُمَّ البَنِين مَا دَجَى الَّليلُ وَغَسَق، وَأَضَاءَ النَّهَارُ وَأَشرَق، وَسَقَاكِ الله مِن رَحِيقٍ مَختُومٍ، يَومَ لايَنفَعُ مَالٌ وَلابَنُون، فَصِرتِ قدوَةً لِلمُؤمِنَاتِ الصَّالِحَاتِ، لأَنَّكِ كَرِيمَة الخَلائِق، عَالِمَةً مُعَلَّمَةً، نَقيَّةً زَكِيَّةً، فَرَضِيَ اللهُ عَنكِ وَأَرضَاكِ، وَلَقَد أَعطَاكِ اللهُ مِن الكَرَامَات البَاهِرَات، حَتَّى أَصبَحتِ بِطَاعَتكِ لله وَلِوَصيِّ الأَوصِيَاء وَحُبّك لِسَيِّدَة النِّسَاء الزَّهرَاءِ، وَفِدَائكِ أَولادكِ الأَربَعَة لِسَيِّدِ الشُّهَدَاء بَابَاً لِلحَوَائِج، فاشفَعِي لِي عِندَ الله بِغُفرَانِ ذُنُوبِي وَكَشفِ ضُرِّي وَقَضَاءِ حَوَائِجِي، فَإنَّ لَكِ عِندَ اللهِ شَأنَاً وَجَاهَاً مَحمُودَاً، وَالسَّلامُ عَلَى أَولَادكِ الشُّهَدَاء، العَبَّاس قَمَرُ بَنِي هَاشِم وبَاب الحَوَائِج، وَعَبد الله وَعُثمَان وَجَعفَر، الَّذِينَ استُشهِدُوا في نُصرَةِ الحُسَينِ بِكَربَلاء، وَالسَّلامُ عَلَى ابنَتكِ الدُّرَّة الزَّاهِرَة الطَّاهِرَة الرَّضيَّة خَدِيجَة، فَجَزَاكِ اللهُ وَجزَاهُم الله جَنَّاتٍ تَجرِي مِن تَحتِهَا الأَنهَارُ خَالِدِينَ فيهَ
By islamicnewupdate.blogspot.com

Comments
Post a Comment