Posts

Showing posts with the label Islamicnewupdate

*Fita Na hudu. GHADEER KUM: WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH??*

  _Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_  Tabbas Manzon Allah Bai Bar Duniya ba Sai daya Nuna Mana Magaji a Bayansa! Saboda an dora masa wani takhlifi, sai ya je wani wuri wanda idan wata masifa za ta sami mutanen Makka, misali ko yaki ko wani bala'i, in ka je ka yi kururuwa ko ka daga sauti ka yi kira, to an san akwai wata magana, watakila an kawo yaki ko wani abu. Da isarsa sai ya hau, yana hawa sai ya ce "ya bani Hashim! Ya bani Abdulmutallib! Ya bani Tim! Ya banu.."/Nan da nan jama'a suka cika wurin makil ya ce musu:"Idan na ba ku labari za ku gaskata? Suka ce haba ya Muhammad!  Ya za a ce ba za mu gaskata ka ba! Bayan ba mu taba samun ka da karya ba." Sai ya ce, "in na ce muku yanzu akwai a bayanBgarin nan mayaka sun taru za su yake ku duk da ba ku gani ba za ku yarda? Suka ce, "za mu yarda, me zai hana? Sai yake cewa, "to ni din nan Manzon Allah ne (S). Daga nan fa sai suka ce "assha! Tir! Don haka ne ma ka tara mu? Sai ya ci gaba da ce...

Fita Na Uku: GHADEER KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH?

_Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_  Zamu cigaba a kashi na biyu Wajibine Shugaba Ya Zama Masanin Abinda Aka Dorashi Akai. ...    Mutum shi kansa ya dubi kansa da kyau in yana da mata da suka fi daya ko biyu da 'ya'ya, to in aka tambaye ka za ka iya tunanin abin da zai je ya dawo. Sai ka ji mutum yana cewa bayan raina na san 'ya'yan nan, imma za a sami matsala, to wane ne. Sai ka ga uba yana kokarin nuna cewa, to ga wane fa suji maganarsa. Wannan amawa (ordinary people) kenan suke fadin haka. Kuma suna iya fahimtar cewa bayansa hadin kai za a samu ko kuma bayan rasuwarsu lalle za a iya samun matsala.    To! Amma sai ga shi kuma shi Ma'aiki (SAW) abin mamaki ya iya barin wannan rayuwar, amma bai tsinkayo wannan matsalar ba, ko kuma ya tsinkayo ta bai sa ma mata magani ba! Shi ne abin da muke fada da kuma manufar ake cewa addinin Musulunci na da shi, to ba ya da shi din Wannan gibim da ake cewa Manzon Allah (SAW) bai cike ba, muna tabbatar da cewa ya cike shi. Kuma han...

Fita Na Biyu: GHADIR KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH (S.A.W)??

 _Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_    Wa͟͟͟͞͞͞j͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞b͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ Ne͟͟͟͞͞͞ Sh͟͟͟͞͞͞u͟͟͟͞͞͞g͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞b͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ya͟͟͟͞͞͞ Za͟͟͟͞͞͞m͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ma͟͟͟͞͞͞s͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞ Ab͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞d͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ak͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Do͟͟͟͞͞͞r͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞s͟͟͟͞͞͞h͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ A Ka͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ {v͟͟͟͞͞͞}.    Kamar yadda muka yi bayanin muhimmancin Shugaba a baya, kuma babu mai musun haka din, to ga shi kuma Manzon Allah (SAW) ya rasu, ashe babu makawa al'ummar wannan Manzon tana bukatar samun wani Jagora wanda zai dora su bisa kan turbar wannan Manzon (SAW).    To, shi kuma wannan Shugaban dole ya san turba din Wannan addini. Misali idan ana son a sa mutum a bisa shugabancin direbobi, idan har ana son ayi adalci, to kamata ya yi a samu wanda ya san mota. Bai kamata ya zamo kenan cewa sai a je asibiti a dauko Likita, wanda ya kware wajen fidar mutum, a ce to ka zo ka zama Shugaban Bakanikan motoci ko na direbobi ba, sannan kuma a dau...

Fita Na Daya: GHADIR KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN MANZON ALLAH??

 _Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_   Muhimmancin Samun Shugaba Cikin Al'umma Abin da zamu iya cewa a nan shine da farko zamu iya cewa sakon wannan addini ba bako bane. Allah (T) tun fil azal ya sunnanta cewa zai rika turo mana da Annabawa saboda wannan kuma ludufi ne na Allah, turo mana Annabawa da zai yi. Amma akwai tuntuni ikirarin da muke yi gaba ga Allah (T) cewa zamu zo mu bauta masa shi daya, saboda mu din nan bayinSa ne. Sai dai bayan zuwan mu duniya muke mantawa, to saboda ludifin Sa ya shiga turo mana da Annabawa domin su zo su tunatar damu kan wannan alkawari da muka yi.    Don haka sai aka fara da Annabi Adam (A.S), daga nan sai wannan yazo ya tafi. Haka-haka, aka yi tayi, ana turo su daya bayan daya, Annabawa daban-daban suna zuwa. To, sai Allah Ta'ala cikin hikima tasa yasa Manzon karshe da zai zo shine Annabi Muhammad (SAW) shine zai zo ya cika shari'a na wannan addini, ya zama bayan Sa babu wata sabuwar shari'ar, bayansa babu wani Annabi da zai zo, zai z...

MUHIMMAN ZANTUKA: INTERVIEW DA SAYYID AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY

Nan kuma wata tattaunawa ce da aka yi da Sayyid Ahmad a munasabar cikar Sayyid Zakzaky shekaru 60 a duniya: Tambaya: Da farko zamu so ka gabatar da kanka ga masu karatu. Amsa: Ni dai sunana Ahmad Ibraheem Zakzaky, sannan nine da na uku a wajen mahaifin mu. Shekaru na 21 koda yake saura wata uku in cika 21 din. Tambaya: Harkokin karatu fa? Amsa: Na kammala sakandare a 2009. Yanzu kuma na samu admission insha Allah a wannan Satumba zan fara degree program dina insha Allah. Tambaya: Da yake muna bukukuwa ne na cikar su Malam shekaru 60, bamu san yadda zaka bayyana mana shi a matsayin Mahaifi a gareku ba? Amsa: To, lalle zan iya tunawa tun ina makarantar secondary School a JSSI, lokacin sai wani malami ya bamu aiki akan mutum ya rubuta bayani akan Babansa, abubuwan da yake son Babansa da shi,  Dakuma matsalolin da yake fuskanta daga Babansa, toni dana zauna zan rubuta wannan aiki din, a lokacin sai na lura cewa ba wani abu da ni zan ce na so da mahaifina yanada shi wanda bai da shi, ba...

NI BA HATSARI NE GA AL'UMMAR KASARNAN BA!, FADIN JAGORAN SHI'A A NIGERIA.

Image
      __________________________ — Sheikh Ibraheem Zakzaky (H): "Nake ce musu, da suke cewa ni hadari ne, misali, to mu gwada mana. Yanzu na san ni zan iya shiga kasuwa na je na yi cefane na fita lafiya lau, amma na san da kyar zan fita kasuwar saboda mutane za su yi ta zuwa suna son mu gaisa. To amma wani Kantoma ko wani Gwamna (ko Ciyaman ko Shugaban kasa) ya je ya shiga kasuwa ba tare da dan sanda ba mu gani. Ya je ya shiga kasuwa shi kadai in bai sha duwatsu ba! Saboda mutane sun san barawo ne, macuci. Ka ga in sun ce ni hadari ne, to ba hadari ne ga mutane ba. Hadari ne ga 'yan fashi, masu mallakar kasa da bakin bindiga. Suna ganin ni hadari ne saboda za su rasa mutane. Sai su ce zai ta da hankali! Hankalin wane ne zai tashi? Na mutanen gari ko na mahukuntan kasa? In na mahukunta ne to dama su basu son gaskiya dole gaskiya ta tada musu hankali." — Shaikh Ibraheem Zakzaky a wani jawabinsa a garin Potiskum shekarun baya.

Jawabin malam turi

Image

INJI SHEAKH YAQUB YAHAYA KATSINA

Image
MALAM (H) MALAMIN DUK DUNIYA NE "Malam Zakzaky ya wuce malaminmu, malamin duniya ne, malam Zakzaky malamin duniya ne malamin al'ummar annabi ne, ya sadaukantar da rayuwa, ya sadaukantar da kuruciya, ya sadaukantar da iyali, ya sadaukantar da dukiya, ya sadaukantar da abin hawa, ya sadaukantar da litittifai, ya sadaukantar da makaranta, ya sadaukantar da komai saboda ya nunama musulmi haka sakon annabi yake. Kulla'as'alakum alaihi ajaran illal mawaddati fil kurba. Ba don a biya malam lada ba, wake da ladan da zai biya malam? Gatan da malam yaima al'ummar nan wake da ladan da zai biya shi, hatta azzaluman da suka kama malam suke zaluntar shi suna bukatar malam wallahi! — Sheikh Yakubu Yahaya wajen rufe Muzaharar Maulud a garin Katsina jiya Lahadi. #FREEZAKZAKY