Fita Na Biyu: GHADIR KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH (S.A.W)??


 _Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_

   Wa͟͟͟͞͞͞j͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞b͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ Ne͟͟͟͞͞͞ Sh͟͟͟͞͞͞u͟͟͟͞͞͞g͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞b͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ya͟͟͟͞͞͞ Za͟͟͟͞͞͞m͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ma͟͟͟͞͞͞s͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞ Ab͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞n͟͟͟͞͞͞d͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Ak͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞ Do͟͟͟͞͞͞r͟͟͟͞͞͞a͟͟͟͞͞͞s͟͟͟͞͞͞h͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ A Ka͟͟͟͞͞͞i͟͟͟͞͞͞ {v͟͟͟͞͞͞}. 

  Kamar yadda muka yi bayanin muhimmancin Shugaba a baya, kuma babu mai musun haka din, to ga shi kuma Manzon Allah (SAW) ya rasu, ashe babu makawa al'ummar wannan Manzon tana bukatar samun wani Jagora wanda zai dora su bisa kan turbar wannan Manzon (SAW). 

  To, shi kuma wannan Shugaban dole ya san turba din Wannan addini. Misali idan ana son a sa mutum a bisa shugabancin direbobi, idan har ana son ayi adalci, to kamata ya yi a samu wanda ya san mota. Bai kamata ya zamo kenan cewa sai a je asibiti a dauko Likita, wanda ya kware wajen fidar mutum, a ce to ka zo ka zama Shugaban Bakanikan motoci ko na direbobi ba, sannan kuma a dauko Shugaban masu karban kudi na kofar get, sai a mai da shi cikin likitoci a ce ka zama Shugabansu! Wannan ka ga ai ba zai yi tsari ba. Wajibi ne Shugaban da ake tafiya a kai, ya zama ya fi kowa sanin abin, sannan kuma ya zama ya fi kowa iya yin abin, da kuma adalci ma abin. 

  To, sai ya zama wai cewa Manzo (SAW) Allah ya dauki ransa ba wasiyya, ba Magaji. Bisa tarihin duk wani mutum mai cikakken hankali da kamala, ba a taba samun ya yi wannan ba: wannan kuwa ba wai sai lallei musulmi ba. Idan mutum ya karanci litiytafan tarihi wadanda ake ce musu manya-manyan mutane a duniya, wadannan mutanen kuwa a Kiristanci ne ko addinin Budha ko ma na al'adu ne ko ma menene, akan samu wasu mutane da suke da wadansu irin baiwa ta musamman, ko wajen Sarauta, ko wajen wani irin ilimi na wani abu daban, to dukkansu, wanda yake tare da wasu jama'a, wanda ya kai a fadi sunansa, to ba a taba samun wanda shi kenan kawai, sai ya rasu ya bar mutanensa haka kawai ba!!

 Dukkansu sai an samu sun rubuta wani rubutu ko sun fadi wata magana cewa bayansu, to jama'arsu ko shugabancinsu ko kungiyarsu sun bar shi a hannun wane. Wannan kuma ko a yanzu halin da muke ciki ka ga cewa duk Sarki in ya kai Sarki, to cikin biyu za ai daya, ko dai ya fito kai tsaye yace bayana ku nada wane ko kuma sai ya yi kokari ya bi ta hanyar masu nadin sarautar nan ya yi musu nuni zuwa ga wani wanda yake so. Sai ka ga bayansa ana ta kokari a kai ga nada wannan wanda yake son nan. Shi yasa ma a kasashen Larabawa za ka ga cewa nan da nan za a ayyana wanda bayan mutuwan wane, ga wane. Shi ne ake ce masa Yarima. Sannan ma yanzu sun ci gaba banda Yarima har ma akwai Yarima na biyu. Sai kaga ga Sarki nan, ga kuma mai jiran gado. 

  To wani lokaci ma Yariman yana iya mutuwa ya bar Sarkin. Wasu wurare ma za ka samu Yarima na biyu, Yarima na uku aka tsara. Wannan me yake muna mana? Yana nuna mana al'amarin shugabanci, al'amari ne wanda kullum gidan rigima ne: amma saboda su magance rigima bayan mutuwarsu Sarakunan kasashen Larabawa suke nada Yarimansu. Tun suna da rai, to ga mai jiran gadonsu, bayansa ga wane, bayansa ga wane. Suna rasuwa shi kenan ba wani ja-in-ja, shi kenan sai ya hau. Abin mamaki a nan, wannan al'amarin da irin su Fahd na Saudiya da sarakunan da muke da su nan, suka iya riskan hadarin su mutu su bar baya ba tare da sun nada Shugaba ba, amma wai sai Manzon Allah (SAW) ne ya kasa gano akwai hadarin in ya tafi ya bar al'umma bai nada Shugaba ba; shi sai ya rasu kawai ba wani Shugaba!!

 Wa iyazubillah. Alhali har wadanda ba musulmi ba sun kai natijan sanin cewa babu wani mutum wanda aka taba samu a tarihin duniya mai hangen nesa kamar Manzo Muhammad (SAW). Mu hadu a kashi na biyunsa (v).

©Media Forum Saminaka
 ```-03|08|2029```

Post--islamicnewupdate.

Comments

Popular posts from this blog

Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali

دعاء المشلول‌

Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa