Fita Na Uku: GHADEER KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH?
_Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_
Zamu cigaba a kashi na biyu Wajibine Shugaba Ya Zama Masanin Abinda Aka Dorashi Akai. ...
Mutum shi kansa ya dubi kansa da kyau in yana da mata da suka fi daya ko biyu da 'ya'ya, to in aka tambaye ka za ka iya tunanin abin da zai je ya dawo. Sai ka ji mutum yana cewa bayan raina na san 'ya'yan nan, imma za a sami matsala, to wane ne. Sai ka ga uba yana kokarin nuna cewa, to ga wane fa suji maganarsa. Wannan amawa (ordinary people) kenan suke fadin haka. Kuma suna iya fahimtar cewa bayansa hadin kai za a samu ko kuma bayan rasuwarsu lalle za a iya samun matsala.
To! Amma sai ga shi kuma shi Ma'aiki (SAW) abin mamaki ya iya barin wannan rayuwar, amma bai tsinkayo wannan matsalar ba, ko kuma ya tsinkayo ta bai sa ma mata magani ba! Shi ne abin da muke fada da kuma manufar ake cewa addinin Musulunci na da shi, to ba ya da shi din Wannan gibim da ake cewa Manzon Allah (SAW) bai cike ba, muna tabbatar da cewa ya cike shi. Kuma hangen nan da wadannan Sarakuna suke hangowa su magance shi, shi ne muke tabbatarwa cewa lalle shi ma Manzon Allah (SAW) ya samu kammala ta, kuma shi ma ya hango kuma ya magance ta.
Wannan shine babban darasin tuna wannan ranar da ake cewa YAUMUL GHADIR. Domin ya zamanto cewa wannan gibi da wannan nakasu da ake ganin kamar akwai ta, mu tabbatar cewa babu ita ga wannan addini, kuma babu ita tare da Manzon Allah (SAW). Wai ya zamanto ya kasa fahimtar cewa wadannan jama'a da yake tara su, idan ya rasu bai fadi makomarsu a baya ba, sai a zo ayi yakin Siffin, ayi yakin Jamal, a yi yakin kaza da kaza, abubuwan da suka faru sannan a ce wai Manzon Allah (SAW) bai kirdado wannan ba, alhali muna karanta cewa wani Sahabi yana fada cewa: "Babu wani abu da zai faru bayan Manzon Allah (SAW) wanda zai kusantar da mu zuwa Aljanah face sai da ya fada mana shi, babu wani abu da zai nisanta mu da wuta face sai da ya gaya mana shi."
Labarurruka da dama da ya fade suna wadanda ma ba daulolin Musulunci ba, cewa bayansa za a yi kaza, za ka gan su a cikin hadisai. Kamar "sa takunu alaikum min ba'adi kaza, kaza." sai a ce kaza zai faru ko kuma kuji ya ce: "innama akhafu wa akhafu alaikum min ba'adi... Da dai sauran irin wadannan zantuttuka, su girgizan kasa har zuwa tashin kiyama. Ranar tashin kiyama ce kadai ya ki ya fada. Wannan ma saboda Allah (SAW) ya nufi boye ta. Har sarakunan da za a yi masu mulki sai da Manzon Allah (SAW) ya fade su. Duk da haka sai wai akwai wasu matsalolin da suka dabaibaye wannan addini, suka faru, sai ake kokarin tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) bai yi magana a kansu ba!!
Wannan abin kuwa shi ne, waye Shugaban musulmi bayan Manzon Allah (SAW)? Shi ne ake samun matsala kan cewa Manzon Allah (SAW) ya yi shiru bai ce komai ba, amma ya yi magana kan yadda za ka yi Sallah, Azumi, Zakka, Haji. yadda za ka shiga bayan gida, yadda mutum zai kwanta da matarsa. Don dai kar ya bar al'umma cikin duhu, sai ya ce ka yi wasa da ita, ka jawo mata sha'awarta, sannan ka kusance ta. In ka je wanka ga inda za ka yi dabsauransu. Komai na addinin nan sai kaga babinsa, amma waye Shugaban musulmi bayan ya rasu? Shi ne Manzon Allah (SAW) bai fadi komai ba, ya bari al'umman musulmi suka ta yin rikici bayansa.
Shi ne muke cewa abin ba haka bane. Manzon Allah (SAW) ya yi magana a kan wannan ma. Alhali mun san shugabanci ya fi zuwa yin bayan gida muhimmanci, shugabanci ya fi cin tuwo muhimmanci, amma duk wadannan wadanda ba muhimmai ba ya yi magana a kai, amma muhimmin bayan ya tafi, yaya rikicin waye zai zama magajinsa, shi ne bai yi magana a kai ba' To. wannan wata matsala ce, wadda take da girman da kuma muhimmancin da dole ya zama cewa gibin da ake ganin ba ta, mu tabbatar da cewa a'a tana nan. Mu hadu ana fita na Uku mai taken; "TABBAS MANZON ALLAH YA RASU YA BAR MANA MAGAJI" -
©Media Forum Saminaka
```-04|08|2020```
https://Islamic new update.blogspot.org.com
Comments
Post a Comment