*Fita Na hudu. GHADEER KUM: WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH??*

 

_Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_


 Tabbas Manzon Allah Bai Bar Duniya ba Sai daya Nuna Mana Magaji a Bayansa! Saboda an dora masa wani takhlifi, sai ya je wani wuri wanda idan wata masifa za ta sami mutanen Makka, misali ko yaki ko wani bala'i, in ka je ka yi kururuwa ko ka daga sauti ka yi kira, to an san akwai wata magana, watakila an kawo yaki ko wani abu. Da isarsa sai ya hau, yana hawa sai ya ce "ya bani Hashim! Ya bani Abdulmutallib! Ya bani Tim! Ya banu.."/Nan da nan jama'a suka cika wurin makil ya ce musu:"Idan na ba ku labari za ku gaskata? Suka ce haba ya Muhammad!


 Ya za a ce ba za mu gaskata ka ba! Bayan ba mu taba samun ka da karya ba." Sai ya ce, "in na ce muku yanzu akwai a bayanBgarin nan mayaka sun taru za su yake ku duk da ba ku gani ba za ku yarda? Suka ce, "za mu yarda, me zai hana? Sai yake cewa, "to ni din nan Manzon Allah ne (S). Daga nan fa sai suka ce "assha! Tir! Don haka ne ma ka tara mu? Sai ya ci gaba da cewa wanene a cikinku zai zo ya taimake ni a kan wannan al'amar da nake a kai na cewa ni Manzon Allah (SAW) ne?"


 A wannan lokacin kuwa kaninsa Aliyu Ibn Abi Talib (A.S) yana wurin. A wata ruwaya ma an ce ya sa (shi Manzon Allah) an nemo gari, an dan yi abinci, an sa a kwano, wanda in ka gani da kyar mutum biyu za su ci, to mutanen da suka taru sun fi arba'in sai aka bai wa wannan ya ci ya koshi, aka bai wa wani ya ci ya koshi. Daya bayan daya sai da duk suka ci suka rage aka ajiye saura. Ya yi haka ne kuma don ya runa musu wata mu'ujiza, don in ya fadi magana su yarda. (Ga abincin da bai wuci mutum daya ko biyu su ce ba. amma sama da arba'in sun ci har sun rage, sannan sai ya gaya musu.


  Don haka sai Aliyu lbn Abi Talib (A.S) ya daga hannu lokacin da Manzo yake cewa: "Man minkum yu'azirruni ala hazal amr, bi shardin an yakuna akhi wa wasiyyi wa khalifati fiikun min ba'adi? Ma'ana. wanene a cikinku zai taimake ni kan wannan al'anmari da sharadin ya zama dan uwana kuma ya zama Khalifana bayana?" Sai duk sukayi shiru. Aliyu (A.S) yana yaro dan shekara bakwai a lokacin ko tara a wata ruwaya, nan take ya daga hannu ya ce. "ha'ana ya rasulallah!" Sai Manzon Allah (SAW) ya kama hannunsa ya saukar.


 Ya sake fada, shiru kake ji. Sai Aliyu (A.S) ya sake daga hannunsa ya ce "Ha'ana ya rasulullah! Sai da Manzo (SAW) yayi haka sau uku. Ana ukun ne sai Manzo (SAW) ya daga hannunsa ya ce: "Hazha akhi, wa wazir wa wasiyyi wa khalifati fikum min ba'adi. fasma'u lahu wa adi'un. Ma'ana ya ce: "Daga yau wannan dan uwana ne. shi ne wasiyyina kuma mataimakina ku bi shi." Nan take sai suka fashe da dariya suna cewa, "ka ji yana cewa shi Annabi ne ba mu ma yarda ba har ya dawo kuma yana nada mana kaninsa wai halifansa a bayansa.


*Ziyarci Shafin Mu Na Facebook*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=121810892949743&id=109956400801859&sfnsn=scwspmo


 In mutum yana son karin bayani ya je ya dubi Littafin Tarikhul Dabari ko kuma mutum ya dauki duk wani tafsirin da yake 'mutayassara' a wurinsa ya duba wannan aya da take cewa: "wa'anzir ashiratakal akrabina," zai ga wannan hadisin. Sai dai akwai ruwaya kamar Ibn Kathir da ya kawo wannan hadisin, sai ya ce Manzon Allah (SAW), akhaza biyadi Aliyu (A.S) wa kala haza akhi wa kaza wa kaza wa kaza..." Ruwayan daya kawo kenan ya ce: "Wannan/dan uwana ne da kaza da kaza. To kaza da kaza da kaza din in ka je ruwayoyi da dama za ka gane abin da yake nufi. Shi ne 'haza akhi wa wasiyyi wa waziri wa khalifati min ba'adi, fasma'u lahu wa'adi'un.


 Dubi irin wannan ta'akidin mai muhimmanci gaske. Tun farko-farkon Risala na Annabci, Manzon Allah (SAW) ya fahimci cewa dole ya zama al'amarin rayuwa sai an sami Shugaba. Wata rana wani Balaraben kauye ya zo daga Jeji ya sami Manzon Allah (SAW) ya ce: "na ji labarinka ne na zo ka yi min bayanin Musulunci. Sai Manzo yake cewa: 'ka shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, ka yi kaza, ka yi kaza.. Sai Balaraben ya ce, "bayan na yi wannan kuma yaya bayanka? Saboda a cikin dabi'a ta Larabawa wani abu ne sananne duk mutum in an same shi a kan wani al'amari, to dole akan abin nan da yake yi ya zama yana da khalifansa.


 To. Larabawa sun san wannan. a gida bayan Ubangida akwai Khalifa, a rayuwa da al'umma da dabi'a da ma komai wani abu ne sananne. Nakasu ne ga Shugaban wasu mutane ya fadi ya rasu bai nada wanda zai gaje shi ba. To. in an yi ta rikici shi za zarga. Sai ya zama kenan Manzon Allah (SAW) da ya gaya wa wannan mutumin Musulunci sai mutumin yake cewa "to bayanka fa a kan wane za ka bar mu? Sai Manzon Allah (SAW) ya yi nuni zuwa ga Aliyu Bn Abi Talib (A.S). Don haka a lokacin sai wasu mutane suka rika cewa, "ka ga tun abu bai tabbata ba yana kokarin nada dan uwansa. Lokacin sai wannan aya ta sauka. Insha Allahu zamu cigaba. 


©Media Forum Saminaka

```-04|08|2020```

https://Islamicnewupdate.blogspot. org.com

Comments

Popular posts from this blog

Tawagar Jonathan ta gana da hamɓararren shugaban Mali

دعاء المشلول‌

Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa