MUHIMMAN ZANTUKA: INTERVIEW DA SAYYID AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY
Nan kuma wata tattaunawa ce da aka yi da Sayyid Ahmad a munasabar cikar Sayyid Zakzaky shekaru 60 a duniya:
Tambaya: Da farko zamu so ka gabatar da kanka ga masu karatu.
Amsa: Ni dai sunana Ahmad Ibraheem Zakzaky, sannan nine da na uku a wajen mahaifin mu. Shekaru na 21 koda yake saura wata uku in cika 21 din.
Tambaya: Harkokin karatu fa?
Amsa: Na kammala sakandare a 2009. Yanzu kuma na samu admission insha Allah a wannan Satumba zan fara degree program dina insha Allah.
Tambaya: Da yake muna bukukuwa ne na cikar su Malam shekaru 60, bamu san yadda zaka bayyana mana shi a matsayin Mahaifi a gareku ba?
Amsa: To, lalle zan iya tunawa tun ina makarantar secondary School a JSSI, lokacin sai wani malami ya bamu aiki akan mutum ya rubuta bayani akan Babansa, abubuwan da yake son Babansa da shi, Dakuma matsalolin da yake fuskanta daga Babansa, toni dana zauna zan rubuta wannan aiki din, a lokacin sai na lura cewa ba wani abu da ni zan ce na so da mahaifina yanada shi wanda bai da shi, ba kuma wani wuri da zance ina da matsala da shi a wuri kaza. Sai dai kawai in rubuta yabo gaba daya, ina ganin ba zasu yarda ba. A lokacin sai na ga idan na rubuta masa wanene mahaifina sai na ga lalle ba zai yarda ba, Sai na rubuta gaskiyar abinda na sani a haka din. Amma daga karshe Sai muka yi ta gardama da shi malamin. Har nake ce masa lalle mahaifina kam ya fita daban. Don haka a interview kamar wannan, ace in fadi wanene shi, kuma ya yake gare ni, gaskiya ba zai yiwu ba. Sai dai wani abu ne idan akace in rubuta littafi mai gima, mai kamar volume biyu zuwa uku, to lalle zai samu. Na farko matsayin sa a wajena. Yana da matsayi na uba wanda ya kammala sharuddan zama uba a wajena. Yana da matsayı na Malami wanda na zauna nayi karatu a gabansa. Sannan kuma yana da karin matsayi na uku shine shugaba a wajena. Ka san ba kowane shugabanka bane malaminka. Sai ka ajiye littafi a gabansa kayi karatu sannan ya zama malaminka a karatu. To, ni bani da malam banda shi, a gabansa na ajiye littafi nake karatun addini. Kamar yadda nace kuma shi mahaifine wanda ya cika sharuddan zama mahaifi, ta yadda ya zama ba wani hakki da dukkan mu zamu nema a wajensa face ya sauke wannan nauyin. Ta yadda ya zama wani'Unique'. Ba in da zaka 6ullo kace yayi maka laifi. Ba kuma ta in da zaku duba ku kwatanta shi da wani. Don haka ya cika dukkan sharud da na zama uba. A matsayinsa na Malami kumma wanda ilmin da zaka samu a wajensa ba wajen wanda zaka je ka samu. Matsayinsa na shugaba wanda yake da hakkin ayi masa biyayya. Ba kowane shugaba bane yake da hakkin ayi masa biyayya ba. Ni a wajena wannan mahaifin nawa idan ina yi masa biyayya, ba ina yi masa biyayya, ba a matsayinsa kawai na mahaifi na ba, ina yi masa biyayya ne a matsayinsa na shugabana. Idan ya umurce ni ina daukar umarnin nan da girma. Ji nake kamar Ka'im (AF) ne yace in yi kaza. Saboda wasu abubuwa idan aka ce in ba da bayani zai zama mai wahala a gareni.A cikin dukkan wadannan abubuwan guda uku dana fada kowannensu za'ayı Magana mai fadin gaske a kansu. Don haka bayani akansa za zama bayani da zai dauki lokaci mai tsawo ana yi.
Tambaya: Zaka bayyana mana yadda kai ka san shi?
Amsa: Lalle idan zan yi bayani yanda ni na san shi, zai zama shi ba mai sauki ba, zan iya cewa yau ina da shekara 12 cikin hankalina, ba zan iya bayar da bayanin baya can sosai ba. Duk da yake akwai wata baiwa, wadanda suka san Abba (Malam) sun san yana da wannan baiwar, yana iya tunawa da abubuwan da suka faru tun yana shekaru uku, shekara hudu, lalle nima haka. Misalı, a lokacin waki'ar Abacha, lokacin da aka kama Abba da sauran abubuwan da suka faru, zan iya zayyano su kamar yanzu, duk da lokacin ina da shekara uku, hudu, biyar ne. Don haka kamar yadda na ce Abba ya cika sharuddan uba a gare mu, na san cewa da yake ni ina da kani, sai ya zama an haife shi shekara daya bayan an haife ni, sai ya zama ni an yaye ni Kafin lokacn daya kamata ya zama an yayeni. Sai ya zama ni an yaye ni kafin lokacin daya kamata ya zama an yayeni. Sai ya zama hidimomin da uwa ke yiwa da, sai ya zama umma tana ji da Kanina, sai ya zama ni kuma Abba ne yake ji dani. Sai ya zama da wanka da duk wasu abubuwan da ka san uwa tana yiwa yaro, a lokacin ya zama Abba yake min. Har ya zama nafi sabawa dashi Abban fiye da Umman, Lalle a sanina da Mahaifina har ya zuwa wannan lokacin, ban taba samun sa a wani hali ko a wani yanayi da yake aikata wani abu ba face wannan abin zallar ibada ne ga Allah. In ka ga ya kwanta barci, a tunaninsa zai tashi, in ya tashi wace ibada zai yi. Don mu muna mamaki, domin ka ga yanayin shekarunsa, mu da muke ganin muna dajini ajika zamu ga kamar zamu fi iya hana ido barci, to amma kuma sai ya zama mun yi barci bai yi ba, mun tashi idonsa biyu. Kuma a wannan yanayin gaba daya yinin za'a tafin dashi ne wajen hidima ga addinin Allah. Cikin dare gaba dayaza'a tafi dashi ne wajen hidima ga addinin Allah. Babu wani lokaci da zaka same shi kace wannan abin daka same shi a matsayın ba ibada bane, lalle ko dai dai da second daya zaka same shi yana yin wani aiki ne na ibada. Ba kuma a lokacin da yake yine kawai ba, in da ka tambaye shi next ya san me zai yi, har zuwa karewar wannan yinin da abinda zai biyo baya. Yana nizamanta al'amuransa. Ni dai abinda zan fada a yana yin da ni na san shi ke nan.
Tambaya: Bayanin daka yi mana ya nuna Malam mutum ne mai hidimomi, ban sanı ba kuna samun damar yin karatu da Malam
kuwa,ko kuwa ya dora wa wani nauyin kula da karantar daku ne?
Amsa: Ya sama mana Malaman dake koyar damu karatun Alkur'ani da yawa. Kusan zan iya cewa dan farawa ne muka yi dashi,
amma dai karatun da na yi zuwa saukewa shi Abba baya gida, don haka da wasu muke yin karatun. Amma yawancin karatun fikhu da muka yi, da shi muka yi, muna karanta Aqa'id dashi, da kuma kadan daga Mandiq. Ina ganin wadannan fannonin na kiyaye lalle sources dina gaba daya har ya zuwa yau a wajen Abba ne, ban Je wajen Wani ba. Lalle ba wani da na ajiye littafi na yi wannan karatun a gabansi sai shi.
Tambaya: Duk da yake kace lokacin da akayi wakiar/Abacha ta faru kana yaro, amma zaka iya tuna wasu abubuwa. 10, zaka gaya mana yadda wannan waki'ar ta zo maku?
Amsa: To, lalle abinda zan iya tunawa ya fara faruwa, na tashi daga barci bayan su Abba sun yi sallar subahi ya shigo, sai na lura yana yin gidan ya dan canza haka, kuma aka ce kar mu fita Ban fahimci menene ba sai lokacin dana leka sai na ga wasu mutane da bindigoginsu haka. To, a wannan lokacin ga 'yan uwa sun yi carko-carko, ba'a san menene ba. Har suka shigo cikin gida suna bincike. Abba yana zagayawa dasu cikin gidan, mu muna kallo. Har suka gama bincikensu suka fita. Har zuwa lokacin, sai na ji wasu sistoci Suna fadin cewa an harbi Malam! Dani da Kanina sai muka rugo da gudu. Muna fitowa sai mukaga Abba, sai yace mana mu koma gida. Sai muka koma. Ni dai ina ganin wannan shine ganin karshe da nayi masa kafin su wuce dashi. Daga nan sai abubuwa suka yi ta faruwa. Domin ba jimawa sai aka zo aka tashe mu a wannan gidan da muke. Sai ya zama an nemi gidan da zamu zauna an rasa, sai ya zama wani malamin umma, wanda ya karantar da ita a makarantar sakandire, sai ya bata gidan haya. A wannan gidan kuma sun rika zuwa suna kawo mana hari, ta yadda zasu zo su balle kofar gidan,su shigo Suyi buge-buge, su mangare wannan, su fasa wancan, su kwakkwashi abubuwa su fita. To, wannan an yi shi akai-akai. Wani abin dariya ma shine, har kanina shi ya dauka irin 'wannän harin ana kaiwa gidan kowa ne, idan suka kawo hari gidanmu, idan mun je makaranta sai ya rika tambayan abokansa a makaranta, kuma jiya an kawo maku harin? Sai ya zama su basu ma fahimci abinda yake cewa ba. Amma dai shi sai ya rinka tambayar Su kojiya an kawo hari? Idan sun zo sai su yi barna ya Zama Sun fita, har ya zuwa lokacin daya zama muna da mai yi mana lesson a gida, da yake gidan yana kusa da dutse ne, idan yazo sai ya hau samah dutsen ya bugi kofar gidan sai mugane cewa yazo, sai mu fita mu gangara wata makarantar firamarı dake kusa da wajen, shima sai ya gangara. ldan mun yi lesson din shi sai ya wuce daga can, mu kuma sai mu dawo gida. Domin idan aka tarar da mutum a kofar gidan ana Kama shi. Akwai wanda ma sanadiyar ganin sa a kofar gidan suka yi sanadiyar shahadarsa. Lokacin ya kawo Almizan ne, da suka ganshi sai suka bishi daga nan dai har suka kama shi, wajen azabtar dashi da suka yi kuma yayi shahada. Haka muka zauna a wannan yana yin na tsawon lokaci. Yadda akwai wani lokaci da' muka fita ni da Yaya Muhammad, muka je filin wani kwallo, mun zauna muna kallon kwallon da yara sa'anninmu suke yi, sai wani yace ai yayan Alzakzaky ne! Sai kawai aka tarwatse, har da 'yan kwallon da 'yan kallon kowa ya gudu, sai aka bar mu mu kadai a wajen. Sai muka tashi muka dawo gida. Sai ya zama wannan yanayin yasa mun shiga wani yanayi wanda yasa hankalinmu ya fita daban dana sauran tsararrakinmu. Gaskiya ni dai nasan wannan yanayin yasa na fita daban da sauran sa'o'ina a shekaru. To,
yanayin ya haifar da cewa Ko a makaranta ma ba za'ayi wasa da mutum ba. Sai ya zama na zama bare na fita daga cikin sa'annina, sai ya zama ina tunani sama da na shekaruna. Ya zama har na iya fanimtar menene yake faruwa damu? Menene yasa muka zama daban duk sauran mutane Sai ya zama ina tunanin cewa wato saboda Harkar Addini ne yasa ake ta kawo mana hari, yasa mutane suna tsangwamar mu. Sai ya zama a wannan lokacin lalle idan aka gwada mu da sa'o'inmu a tunani sai ya zama zamu iya kallon su a matsayin yara saboda tunaninmu na gaba da nasu.
Tambaya: Zaka gaya mana yadda aka kama Malama Zeenah a wannan lokacin?
Amsa: Wannan malamin namu dana ce maka yana wurga dutse idan yazo yi mana lesson, a wannan ranar sai muka ji an buga
kofar kamar yadda ya sabayı. Sai muka ce ga Malam Tukur yazo, bari mu fita. Ashe sun zo ne, ni dai ban san yadda akayi a wannan lokacin muka ji kwankwasar kadan ba. Domin idan sun zo da karfin tsiya suke shigowa. Daga nan sai muka ji sun fara buga kofar garam-garam. Lokacin har sunyi harbi sama. Dama sun saba idan sun zo sukan harba tiya gas shine yasa kanina yake da wata matsala ko da yake yanzu ta warware, yana da wani irin tari,wanda yanayin tarin yasa ake ganin kamar ba zai yi rai ba lokacin. Sai ya zama wadannan
yaran, sanadiyyar wannan tiya gas din da ake yawan jefawa a sama na nan na takura masu. Wannan harin da suka kawo, suka ballo Kofar da karfin tsiya, Wanda yafi kowa shan tiya gas din Mahmud kenan lokacin yana tsakar gida, da suka danno sai nake cewa Hamid, lalle Mahmud yana
can, sai na fita waje. Ina fita sai na gan shi a kwance ga tiyagas din a gefensa haka. Na nufi in da yake in dauko shi sai naji kawai yanayin hayakin tiyagas din, sai ya sa naji na rasa Karfi, sai nima na fadi a wajen. Koda yake ni dai ban rasa ganina ba, don ina gani, amma bana iya motsi. Sai wani dan sanda ya ballo kofar ya shigo, ya Kama ni da Mahmud din yajamu, sai ya fita damu ya wurga mu a mota. muna nan Sai aka fito da Umma da duk sauran mata da yaran dake cikin gidan.A lokacin ni dai jikina ba karfi. Don ina da wani tabo har yanzu gashi nan. gugan tsinin dake bakin bindiga ne. Sai ya zama a lokacin akwai wani abu da ya faru wanda har yau idan na tuno yana bakanta min rai, shine, dukkan mu aka hada mu a cikin mota, sai ya zama mahaifiyar mu tana kabbara, sai suke cewa tayi shiru ta daina, sai tace ba zata daina ba, sai wani yasa hannu ya mare ta. Taci gaba da Kabbara, Ina ganin sai da ya mare ta sau uku. Wannan yana cikin abubuwan da koda yaushe na tuno, ba abinda ke hana hawaye fitowa daga idona. Kuma a duk abinda ya faru ba abinda ke bakanta min rai Kaman wannan. Ta yadda ya zama da farko dai ni inda a ce na wuce wannan shekarun, bai zai yiwu ina da rai ayi haka nan ba. Na biyu kuma a wannan lokacin bana iya motsa jikina. Sai ya zama ina kallo akayi haka nan, amma babu abinda zan ya yi. Da muka zo aka kai mu police station, anan ma ta cigaba da kabbara, mu an ajiye mu a bayan Kanta ne, aka shiga da ita ciki, muna jin tana kabbara, sai suka samo mata'yan sanda suna ta dukan ta, data fito ne take ce mana duk jikinta nayi mata ciwo, yayi tauri ma Kamar dutse. A haka dai muka zauna Daga baya suka yi ta caccanza mana police station, har daga baya suka so su kaimu kurkuku, wadoji suka ce ba zasu karbe mu ba, daga baya suka dawo damu hedikwata, lna ganin mun zauna a police station din Tudun Wada, mun zauna a hedikwata, sannan mun zauna a Dan Magaji.
A duk wannan yanayin abubuwa da yawa sun faru, wanda bayaninsa zai zama dogon bayani ne mai tsawo sosai. Amma dai abinda ya faru a ce mutum yana da kamar shekara hudu yaga duk wadannan abubuwan sun faru dashi, yasan cewa lalle tun farko rayuwarsa ba a kawo shi domin wani abu kamar yadda kowa yadauka yazo yi ba. Don haka ni na fahimci cewa tun farko dama an sara rayuwar mutum ne domin hidima ga addinin Allah ne, ta yadda ya zama an fara fuskantar jarabawa tun kafin asan menene jarabawan an fara fuskantar wahala tun kafin ma a fahimci me cece wahalar.
Tambaya: Malam ya cika shekara 60, me zaka ce?
Amsa: Lalle muna farin ciki kuma muna rokon Allah ya kara mana damar rayuwa da wannan mahaifi namu shekaru da yawa masu zuwa, saboda duk wata ni'ima da duk wani kwanciyar hankali da jin dadi da muke dashi, ba abinda ya zarce wannan mahaifi namu. Kuma bamu da wani fata, ba gare mu kawai ba, ga yan uwa da al'umma baki daya na samun wani sauyi wanda zai kawo canji na tafarkin da ake bi, ya koma tafarkin Allah da kuma canjimana rayuwar,mun tabbatar ba wani fata daya zarce wannan tafarkin mahaifin namu, Don haka lalle wadannan shekarun abune na farin ciki ba dan kadan ba, kuma abune wanda zamu yi fatan Allah ya kara mana damar rayuwa dashi a Shekaru masu yawa masu zuwa.
Tambaya: Kana da wani kira ga yan uwa?
Amsa: Lalle kiran da zan yi ga yan uwa shine, wani lokaci daga experiences din da nake dashi da Abba, da abinda ya zama ni na sani daga wajensa, lalle ni ina ganin abinda nake zato daga gare shi. Wannan al'amarin sirrin Allah ne, kuma 'yan uwa su sani cewa Malam rahama ne da Allah ya ajiye a tsakaninmu.
©Media Forum Saminaka
-28|07|2020
Comments
Post a Comment