WAFATIN UMMUL BANIN MAHAIFIYAR ABUL FADLIL ABBAS!
Bismillahirrahmanirrahim 13 ga Watan Jumadat-Thaniyah. A irin wannan rana ce a Shekara ta 65 bayan hijirah, a ranar Juma'a, Allah ya karbi ran Ummul Banin (S.A), Mata a wajen Imamu Ali alaihissalam kuma Mahaifiyar Abul Fadlil Abbas Jarumin Karbala!. Tsarkakken Makwancinta yana nan a ciki Makabartar Baqi'a, a kusurwar bangaren hagu kusa da Makwancin Sayyid Ibrahim Dan Ma'aiki (Saww), da Zainab da Ummul Kulthum da Abdullahi da Kasim, amincin Allah ya kara tabbata a gare Su. WACE CE UMMUL BANIN (S.A)? Zanannen Sunanta Shi ne Fadimatu 'Yar Hizam. Mahaifiyarta kuwa ita ce: Thumamah bnt Sahal bn Amir bn Malik bn Ja'afar bn Kilab. Ta kuma Shahara da Lakabin Ummul Banin, kuma an ce Imamu Ali (as) ne da kansa ya kira ta da laqabin na Ummul banin. AURENTA DA IMAMU ALI (AS). Malaman Tarikhi sun ruwaito cewa Imamu Ali (as) ya sanya Dan uwansa Aqil ne da ya nemo masa wata Mace Jaruma daga Gidan Jarumawan Kabilun Larabawa domin ta haifa masa Jarumin da zai agaza wa Dansa Hus...