Fita Na Daya: GHADIR KUM, WAYE SHUGABAN MUSULMI BAYAN MANZON ALLAH??
_Daga: Muh'd Jawad Assaminaky_
Muhimmancin Samun Shugaba Cikin Al'umma Abin da zamu iya cewa a nan shine da farko zamu iya cewa sakon wannan addini ba bako bane. Allah (T) tun fil azal ya sunnanta cewa zai rika turo mana da Annabawa saboda wannan kuma ludufi ne na Allah, turo mana Annabawa da zai yi. Amma akwai tuntuni ikirarin da muke yi gaba ga Allah (T) cewa zamu zo mu bauta masa shi daya, saboda mu din nan bayinSa ne. Sai dai bayan zuwan mu duniya muke mantawa, to saboda ludifin Sa ya shiga turo mana da Annabawa domin su zo su tunatar damu kan wannan alkawari da muka yi.
Don haka sai aka fara da Annabi Adam (A.S), daga nan sai wannan yazo ya tafi. Haka-haka, aka yi tayi, ana turo su daya bayan daya, Annabawa daban-daban suna zuwa. To, sai Allah Ta'ala cikin hikima tasa yasa Manzon karshe da zai zo shine Annabi Muhammad (SAW) shine zai zo ya cika shari'a na wannan addini, ya zama bayan Sa babu wata sabuwar shari'ar, bayansa babu wani Annabi da zai zo, zai zama yayi takmil din addini din ya cika shari'a din.
To, amma bayan Sa kuma duniya din zata tafi tafiya mai tsawo, kuma alhali wannan wani fidra ko kuma muce Sunnah ce da dan Adam bazai taba rayuwa ba sai da shugabanci. Saboda duk wani abu mai tsari bazai tafi ba sai da shugaba; wannan kuma dole ne, kuma addini nan haka ya sunnata mana. Shi yasa ake ce mana ko tafiya za'ayi, idan har mutum sun kai biyu, to dole a samu Shugaba a cikin ku, saboda muhimmancin Shugaba a addini Musulunci.
Yazo a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Izha kuntuna thalathatan fal yu'ammir ahdukum." Ma'ana "Idan kun kasance ku uku (a tafiya), to ku shugabantar da dayan ku." Wannan kuma wani abu ne mai muhimmancin a addini, saboda wani abu mai tsari dole ne yana tafiya tare da shugabanci. Amma idan babu shugaba, wato ya zama taron kazo-nazo kenan amma inda Shugaba kaga kenan abin zai tafi bisa tsari.
Don haka sai ya zama kenan idan Annabi yana nan a cikin al'umma kaga shine shugaban dukkan wasu masu imani, to tunda Annabi (SAW) yazo, zai zama kenan cewa bayan sa babu wani Annabi da zai zo, sannan kuma za'ayi al'ummu da yawan gaske. Misali yanzu daga rasuwar sa zuwa yanzu wajen shekara Dubu da Dari hudu da wani abu, ashe kenan ba zai zamo akwai tsari ba Allah (SWT) ya daura ran Manzon Allah (SAW) sannan a bar al'ummar sa su zauna sama da shekara dubu, amma babu wani shugaba a cikinsu, sai abinda kawai sukayi, an bar musu littafi da yazo musu dashi.
Wannan shine yasa ka dole a dukkan zamani ya zamo dole akwai shugaba mai saita mutane da tunasar dasu addinin Allah. Tunda, ko tafiya mutune biyu zasu yi, sai daya ya zama Shugaba a cikinsu, to inaga in Manzon Allah (S) ya koma ga Allah bai bar magaji (Khalifa) a bayan sa ba? Mu hadu a fita Na biyu mai taken: WAJIN NE SHUGABA YA ZAMA MASANIN ABIN DA AKA DORA SHI A KAI.
©Media Forum Saminaka
```-02|08|2020```
Post - islamicnewupdate
Comments
Post a Comment